Sanata Marafa ya nemi ayi wa masu kokarin murde zaben APC duka a Zamfara

Mun samu labari cewa Jam'iyyar APC mai mulki ta samu kan ta cikin
rikicin cikin gida a Jihar Zamfara a dalilin zaben fitar da 'Dan
takaran Gwamnan Jihar a karkashin APC a zabe mai zuwa 2019. Kamar
yadda labari ya zo mana, rikicin da ake bugawa a Jam'iyyar APC a Jihar
Zamfara yayi mugun kamari inda har ta kai Uwar Jam'iyya ta rusa
shugabancin APC na Jihar a lokacin da ake daf da shirin tsaida 'Dan
takarar Gwamna. Sanata Kabiru Marafa wanda yana cikin masu neman
Gwamna a Zamfara a wani bidiyo da ya shigo hannun mu ya umarci magoya
bayan sa su yi wa duk wanda su kayi kokarin kawo hatsaniya wajen zaben
fitar da gwani na APC. Kabiru Marafa yayi wannan kira ne lokacin da ya
fita yawon kamfe kwanaki inda ya nemi Mutanen sa su takawa duk masu
neman tada rikici a wajen zaben APC burki. Sanatan yace a lakadawa duk
wanda ya zo wajen akwatin zabe duka. Marafa wanda yake wakiltar
Zamfara ta tsakiya a Majalisar Dattawa ya bayyana cewa a shirye yake
Jami'an tsaro su damke sa a sakamakon yi wa masu neman yin magudi a
zaben APC na Jihar Zamfara duka da Masoyan na sa su ka yi. Ana dai sa
rai Jam'iyyar APC za tayi maza ta fitar da 'Dan takarar Gwamna a Jihar
inda Sanata Marafa ya gargadi Jam'iyyar cewa idan tayi sake, za a
tashi APC ba ta da 'Dan takarar Gwamna a Zamfara saboda rikicin da ake
tayi a Jihar. Kwanakin kun samu labari cewa rikici ya barke a Gabashin
Jihar Neja bayan zaben fitar da gwani na Jam'iyyar APC mai mulki inda
Sanatan da ke wakiltar Yankin ya sha kasa a zaben da aka soma.

Hausa.naija.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN