Muryar Amurka ta sallami ma’aikatan sashen Hausa 15, saboda
zargin su da ake yi da rbar kudi da ya sabawa ka’idar aiki wato cin hanci.
Daraktar Muryar Amurka Amanda Bennett ta bayyana ahakan a wani sakon imel da ta
aikewa ma’aikata a ranar Alhamis, 4 ga watakn Oktoba.
Ta bayyana cewa cewa, an shaidawa hukumomin game da zargin
su a cikin "watanni da suka gabata", nan da nan kuma aka kaddamar da
bincike. Tace, “yayinda doka ta hanamu bada bayani daki-daki, bayan kammala
binciken ne aka dauki matakin sallamar ma’aikatan.
" Amanda Bennett tace “wani gwamna ne daga daya daga
cikin wadannan yankunan da Sashen Hausa ke watsa shirye-shiryensa, ya bada
kudin.” Tace an kuma kaddamar da bincike domin tantance ko an watsa wadansu
shirye shirye sabili da kudi da aka karba ne, kuma idan aka tarar da haka, za a
dauki mataki nan take yadda ya kamata.
Bennet tace shugabannin sassan harsunan Afrika na Muryar
Amurka sun bada cikakken goyon baya yayin gudanar da binciken da kuma shawarar
da aka tsayar na sallama ko kuma niyyar sallamar wadanda abin ya shafa.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING?
Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
Hausa.naija.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI