• Labaran yau

  Wani Matashi ya nufi Abuja a kasa daga garin Zaria saboda nasarar Atiku


  Wani maatshi mai suna Kamaludden Bashir ya kama hanyar zuwa babban birnin tarayya Abuja a kasa daga garin Zariya na jahar Kaduna don bayyana farin cikinsa da nasarar da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP ya samu a zaben fidda gwanin jam’iyyar.

  A ranar Litinin Bashiry ya fara wannan tattaki, inda a ranar Talata 9 ga watan Oktoba ya isa garin Kaduna akan hanyarsa ta zuwa Abuja, inda ya bayyana ma manema labaru cewa burinsa shine ya isa Abuja cikin kwanaki biyar.

  “Ina matukar farin ciki da nasarar da Atiku ya samu, wannan ne yasa na kama tattakin zuwa Abuja don na tabbatar masa da cewa ina tare da shi dari bisa dari, haka zalika zan wayar da kawunan dubunnan matasa akan wannan turba ta goyon bayan Atiku domin ya kai kasarnan ga gaci.” Inji shi.

  Malam Bashir wanda ya fara tattakin daga kwarbai dake garin Zaria da misalin karfe 6:30 na safiyar Litinin tare da amincewar iyayensa, ya ce yana da yakinin Atiku ne kadai zai iya shawon kan matsalolin tsaro, talauci, rashin aiki da matsalar rikicin addini da kabilanci. Haka zalika Bashir yace ya gamsu da shirin da Atiku yake yi a duk fadin kasarnan , don haka yace;

  “Na yarda da Atiku shi yasa nake wannan tattaki don goyon bayansa tare da addu’ar Allah ya bashi nasara a zaben 2019, shin mutumin da zai iya yaki da rashawa a Najeriya.” A cewarsa, a tsakanin tafiyar da yayi daga Zaria zuwa Kaduna yan fashin sun kwace masa abincin da yayi guzuri dasu tare da yan kudaden da ya riko a hannunsa, amma duk da haka ba zai karaya ba har sai ya isa garin Abuja domin ya cika burinsa.

  Daga karshe Bashir mai tattaki yayi kira ga sauran matasan Najeriya dasu mara ma Atiku Abubakar baya domin ya kai kasarnan ga tudun mun tsira.
   

  Shafin mu na Facebook web.facebook.com/isyakuweb

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

  Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

  Hausa.naija.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani Matashi ya nufi Abuja a kasa daga garin Zaria saboda nasarar Atiku Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });