Matasan Tijjaniyya sun dau mataki bisa tarko da Yahudawa suka shirya wa matasa. Hotuna

Matasan Darikar Tijjaniyya a garin Birnin kebbi, ranar Asabar, sun gudanar da taron wa'azi a garin Ambursa da ke jihar Kebbi bisa maudu'in jan hankalin samari su daina koyi da halayen Yahudawa, sai kuma nasiha akan sauke nauyin da Allah ya dora ma iyaye a kan 'ya'yansu.Hakazalika nasihar ta kara haske a kan darajar Malamai ga Dalibansu da kuma muhimmancin Darika ga masuyi.

Malamai da suka gabatar da wannan nasiha sun hada da Malam Abdulrahman na Malam Dan Atto Tudun wada Birnin kebbi, sai malam Sani, da Malam Mudassir Muhammad sai Malam Abbashi wanda ya kammala taron wa'azin.

Dattijo Malam Muhammadu Dantuni Sarkin Malaman Amburs, ya gabatar da ta'aliki a kan dukkannnin bagire da aka fadadasu ta hanyar wa'azi daga Malamai da suka gabatar da nasiha. Ya kuma bayar da muhimmanci ga hakkin 'da zuwa ga Mahaifinsa. Malam ya ce " idan ka gan mace tana shiga tsakanin 'da da Uba, bata da arziki, tana son dan ya rasa arziki, ba'a shiga atsakanin 'da da Uba. Ba inda 'da zai je ya sami abu mai amfani matukar ya ketare Uban shi".

Daga karshe,  Limamin Masallacin garin Ambursa ya rufe taro da addu'a, daga bisani aka watse daga wajen taron lafiya.

Ita dai kungiyar Matasan Tijjaniyya ta dau haramar ganin ta ci gaba da gudanar da aikin neman lada tare da neman yardar Allah wajen ganin ta fadakar da Samari da Matasa hanyar gaskiya na addinin Musulunci, musamman dangane da tsarin rayuwa, hulda, ibada, tarbiyya, dogaro da kai duka ta tsarin addinin Musulunci da kuma kara wayar da kan matasan Tijjaniyya falalar Darikar musamman gudanar da lazimi da tare da salati ga Manzon Allah (SAW).


Daga Isyaku Garba

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN