Magoya bayan Mama Taraba 50,000 sun fice daga APC sun koma UDP

Tsohuwar Ministan Harkokin Mata kuma 'yar takarar gwamna karkashin jam'iyyar United Democratic Party (UDP) a jihar Taraba, Sanata Aisha Alhassan wanda akafi sani da Mama Taraba ta karbi magoya bayanta 50,000 da suka baro APC zuwa UDP a ranar Litinin.

A taron karbar sabbin mambobin da aka gudanar a dakin taro na Unity da ke Jalingo, Alhassan ta tabbatarwa magoya bayanta cewar za ayi musu adalci a jam'iyyar UDP. Jagoran wadanda suka sauya shekar kuma tsohon jigo a jam'iyyar APC a jihar, Uba Mairiga ya ce rashin adalci da aka yi masa da magoya bayansa ne ya sa suka fice daga jam'iyyar APC.

Mairiga ya shiga takarar dan majalisar jiha na yankin Jalingo II a APC amma aka kayar da shi a zaben fidda gwani, yanzu kuma ya sake sayan fom din takara na mazabar karkashin jam'iyyar UDP. "Ni da magoya baya na mun baro APC kuma za mu bayar da gudunmawarmu domin ganin UDP ta yi nasara a dukkan zabukkan da za'ayi a jihar," inji shi.

A bangarensa, gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya taya Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar muranar lashe zaben fidda gwani da shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Hausa.naija.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN