Kotu ta yanke ma direba da ya kashe jami'in FRSC a B-kebbi hukuncin kissa

Daga Isyaku Garba 5-10-2018


Wata babbar Kotu a Birnin kebbi na jihar Kebbi, ranar Laraba, ta yanke ma wani Direba mai suna Usman Aliyu hukuncin kisa. Direban wanda aka fi sani da suna "Kwastoma" ya buge wani ma'aikacin hukumar FRSC ne mai suna Muhammad Babangida da gangan, lamari da ya yi sanadin mutuwar jami'an nan take ranar 3 ga watan Aprilu na 2017 kan titin Ahmadu Bello da ke garin Birnin kebbi..


Sanarwar haka ta fito ne daga hannun jami'in hukumar sashen fadakar da al'umma, Bisi Kazeem a garin Birnin kebbi. Ya ce Direban ya tuko wata mota Toyota Corolla mai lamba KLG 342 AA ranar 3 ga watan Aprilu na 2017, kuma bisa bayanai da aka tattara, Direban ya kuduri aniyar buge wani jami'in hukumar ne mai suna Abubakar Garba Abubakar, wanda ke gudanar da aikinsa tare da sauran jami'an hukumar a kan titin Ahmadu Bello.

Amma kasancewa Abubakar ya yi tsalle ya kauce wa motar, duk da haka sai Direba Usman Aliyu ya nufi wajen Babangida ya buge shi har lahira. Daga bisani kuma ya tsere, amma aka kama shi a garin Kalgo bayan an shaida wa 'yansanda abinda ya aikata.

Kotu ta yanke wa Usman Aliyu hukuncin kissa ranar 4 ga watan Oktoba bayan ta kama shi da laifin aikata kissar gilla.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN