Type Here to Get Search Results !

Main event

Kalli sassan jikin Janar M.I. Alkali da aka gano a cikin wata rijiya.Hotuna

An gano gawar Maj.General Muhammed Idris Alkali mai murabus a cikin wani kangon rijiya da ke kauyen Guchwet da ke gundumar Shen a karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Plateau.

ISYAKU.COM ya gano cewa duk da yake babu wani gwaji na Likitanci da ya tabbatar da cewa sassan jiki da aka samu a cikin rijiyar na marigayin ne, amma mahukuntan soji sun ce sun tabbatar da cewa sassan jikinsa ne sakamakon bincike da suka gudanar.

Hakazalika  Brg. Gen Umar Ibrahim, kwamandan Garrison na 3, ya shaida wa manema labarai a wajen da aka gano gawar cewa wadanda suke da hannu wajen kashe Janar Alkali ne suka kawo soji wajen rijiyar da kansu, bayan an cire gawar daga wani kabari da aka fara bizine shi da farko kafin soji su fara nemansa.

Ya kuma ce za'a gudanar da paretin ban girma ga gawar Maj.Gen. M.I Alkali a wajen da aka gano gawarsa da zarar an gama hada sassan jikinsa da aka ciro daga cikin tsohuwar rijiyar. Janar Alkali ya yi batan dabo ne a kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja ranar 3 ga watan Satumba.

DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without expressed permission from us.

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies