Jarage 2 na sojin Sudan sun yi karo a filin jirgin sama na Khartoum

Jirage biyu kirar Antonov An-26 da an Antonov An-32.mallakin hukumar soji na kasar Sudan sun yi karo da juna a babban filin sauka da tashin jiragen sama da ke Khartpum a kasar Sudan.

Jiragen Antonov salon sumfurin kirar tarayyar Soviet, sun sauka ne 'yan dakikoki da juna kafin faruwar lamarin wanda ya faru sakamon saukowa kusan lokaci daya a layin sauka na jiragen, daga bisani kuma suka yi taho mu gama da juna.

Daya jirgin ya kare daga wajen hancinsa  kuma ya rabu gida biyu, mutum takwas sun sami raunuka kuma an kaisu Asibiti domin samun kulawar Likitoci.

Rundunar sojin sama na kasar Sudan dai ta mallaki jirage takwas ne kirar Antonov An-26 da kuma jirage guda shida kirar an Antonov An-32.

Ko a ranar 21 ga watan Satumba, matuka jirargen sama guda biyu sun mutu bayan jiragen yaki biyu sun fadi a kusa da birnin Omdurman da ke kusa da Khartoum a gaban yammacin Rafin Nile. Wannan ya biyo bayan faduwar wani jirgi mai saukar Angulu a Darfur yan kwaanakin baya, amma duk mutane da ke cikin jirgin sun tsira kafir jirgin ya kama da wuta.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

0/Post a Comment/Comments

Rubuta ra ayin ka

Previous Post Next Post