Jami'in crypto coins ya bace da sama da N40m na jama'a a garin Birnin kebbi

Isyaku Garba 31-10-2018

Mutane da dama ne suka shiga matsananciyar damuwa, wasu ma har da fashewa da kuka bayan ranar  Talata a unguwar Tudun wada Birnin kebbi inda ofishin Crypto Coins ke da gindin zama, ana zargin sun gano cewa wakilin Crypto coins wanda aka fi sani da suna Mr Okoro, ya yi batan dabo kuma lambobin wayarsa a kashe, wanda hakan ya sa suka gano cewa Crypto Coins ta damfare su makudan kudadensu ne a garin Birnin kebbi.

ISYAKU.COM ya gano cewa wannan ofishin Crypto Coins an bude shi ne kimanin wata biyu da suka gabata, kuma ya kama ofis a wani gini da ke unguwar Tudun wada a garin Birnin kebbi, karkashin jagorancin wani mai ruwan kabila wanda ake kira da suna Mr. Okoro. Mun gano cewa Crypto Coins tana yi ma jama'a alkawari cewa su zuba kudinsu domin a juya masu kudin wajen kasuwanci da ya shafi, Zinari, Azurfa, Lu'u lu'u da sauransu, daga bisani kuma a ba mutum riban abin da aka samu a saman uwar kudinsa kowane kwana 10.

Wani da bayason a fadi sunansa, kuma ya fada cikin tarkon wannan dan damfara, ya shaida mana cewa " Ni kaina Allah ne ya kaddara na shiga wannan tarko, domin dai na sa N50.000, kuma bayan kwana 10 an bani N3.000 wai kasancewa riba da aka samu da kudi na. Bayan haka, akwai wadanda suka sa fiye da N70.000 da kuma wata mata daga Jega da ta sa fiye da N3m. Abin mamaki shine yadda wannan mutum ya yi batan dabo, kuma aka rufe ofishin".

Binciken mu ya nuna cewa babu wanda ya san asalin inda wannan mutum ya fito, hakazalika, hatta wadanda ya samo suka fara sanar da jama'a cewa an bude wannan ofis, kuma 'yan unguwa, su ma kansu basu san gidan da ya sauka ba a garin Birnin kebbi, balle su san asalin gari ko jihar da Mr Okoro ya fito, wanda zai yi matukar wuya idan har Mr Okoro hakikanin sunansa ne.

Sai dai a tattaunawar mu da kakakin hukumar NSCDC na jihar Kebbi Mr. Bamayi ya tabbatar mana cewa ba wanda ya shigar da kara a hukumar NSCDC dangane da wannan lamari kawo yanu, sai dai jami'ansu na kai kawo a wannan unguwar domin tabbatar da tsaro.

An kiyasta cewa Crypto Coins ta tattara akalla N40m daga hannun mutane a garin Birnin kebbi da kananan hukumomi daga bisani ta yi batan dabo ta bar wadanda suka zuba kudinsu da yin Allah ya isa.

DAGA ISYAKU.COM

Copyright, do not copy and paste our news on your blog without expressed permission from us. 

Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi jihar Kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN