Mun samu rahoton cewa babbar hukumar zabe ta kasa watau
INEC, ta nuna hali irin na dattako wajen tunkarar fusatattun shugabanni na
jam'iyyar adawa ta da suka gudanar da zanga-zanga a gaban ofishinta dake birnin
tarayya na Abuja.
Jiga-jigan jam'iyyar PDP sun aiwatar da zanga-zangar su ta
lumana domin bayyana takaicin su kan dambarwar zaben gwamnan jihar Osun da ya
wakana makon da ya gabata. A sanadiyar haka cikin nuna hali na dattako hukumar
INEC ta tari numfashin kusoshin jam'iyyar ta PDP tare da rarrashin su da
kalamai da lafuzza masu dadi domin kwantar ma su da hankali. Hukumar da sanadin
kwamishinonin ta biyu, May Agbamuche-Mbu da kuma Muhammad Haruna, sun rarrashin
fusatuwar jiga-jigan jam'iyyar ta hanyar bayar da amincinsu kan tabbatar da
gaskiya da adalci yayin gudanar da babban zabe na 2019.
Jiga-jigan jam'iyyar da suka halarci wannan zanga-zanga sun
hadar da; shugaban jam'iyyar na kasa, Prince Uche Secondus, shugaban majalisar
dattawa, Abubakar Bukola Saraki, gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal da kuma
Sanata Kano ta tsakiya, Rabi'u Kwankwaso.
Sauran kusoshin jam'iyyar sun hadar da Sanata Dino Melayet
na jihar Kwara, Sanata Ben Bruce na jihar Bayelsa, tsohon gwamnan jihar Jigawa
Alhaji Sule Lamido da kuma shugaban jami'ar Baza, Datti Baba Ahmed. NAIJ.com ta
ruwaito cewa, a yayin aiwatar da wannan zanga-zanga cikin lumana, hukumar 'yan
sanda ta Najeriya ta kuma tirnike kusoshin jam'iyyar da Barkonon Tsohuwa.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING?
Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
Hausa.naija.ng