• Labaran yau

  Hatsabibi ya kashe tsoho dan shekar 75, ya kashe dansanda da ya je kama shi.Hotuna

  Rundunar 'yansandan jihar Ondo ta damke wani matashi da ake kira “At-all-at-all” bayan ya kashe wani tsoho dan shekara 75 mai suna Mr. Olusegun Oyadele a gonarsa ta hanyar sare shi da adda , daga bisani kuma ya kashe wani jami'in dansanda da ya je domin ya kama shi sakamakon kashe tsoho dan shekara 75 a matsugunin  gona na Onipetesi da ke karamar hukumar Ondo ta yamma.

  Bayanai sun ce tsohon ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake baje diyan amfanin gonarsa na diyan Cocoa kafin “At-all-at-all” ya je ya sassare tsohon da adda da sanyin safiyar Asabar lamari da ya yi sanadin mutuwar wannan tsoho nan take.

  Kakakin hukumar yansanda jihar Ondo Mr Femi Joseph ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce bayan lamarin ya faru, wata mata mai suna Veronica Olawale ta shigar da kara a caji ofis na rundunar yansanda a Enu-owa wanda suka tura yansanda 4 domin su taho da wanda ya yi kisa.

  Amma yayin da daya daga cikin yansandan ya yi kokarin kama shi sai ya sassare dansandan har lahira, sai ya gudu ya shiga gandun daji.

  Daga bisani dai dole aka karo jami'an tsaro tare da hadin guiwa da 'yan banga karkashin jagorancin Kwamishinan yansanda na jihar Ondo Mr. Gbenga Adeyanju aka shiga gandun dajin domin farautar wanda ya yi kisa, kuma daga bisani bayan an share awa 13 ana nemansa a cikin gandun dajin sai aka kama shi a wani gandun daji a kauyen Tekunle da ke Bolorunduro a karamar hukumar Ondo ta gabas.

  Daga sashenmu na jakar magori

  Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

  Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hatsabibi ya kashe tsoho dan shekar 75, ya kashe dansanda da ya je kama shi.Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });