• Labaran yau

  Budurwa ta debo ruwan dafa kanta bayan ta yanke makogoron wata budurwa yayin fada


  Yansanda a birnin Lagos sun damke wata fitinanniyar budurwa mai suna Opeyemi Adamson mai shekara 23 bayan ta yi amfani da wuka ta yake makwabciyarta mai shekara 28 Taiwo Olowookere  da wuka a wuya yayin da suke fada a gidan da suke zaune a unguwar Meiran a birnin Lagos.

  Sakamakon haka Taiwo Olowookere ta yi fama da zubar jini matuka, sakamakon haka makwabta suka garzaya da ita zuwa Asibiti, inda daga bisani kuma ta sheka lahira.

  Tuni dai yansanda daga Meirin suka kama Opeyemi Adamson kuma suka mikata ga babban sashen bincike na yansanda na SCIID da ke Panti a Yaba da ke birnin Lagos.

  Yansanda sun gurfanar da Opeyemi Adamson a gaban Kotun Majistare da ke Ebute Metta bisa tuhumar kisan kai. Alkalin Kotu Mr. A.O. Komolafe bai aminta da lamuni da Opeyemi Adamson ta bukata ba, sakamakon haka ya tura ta Kurkuku kafin a sami alkiblar da shari'arta zai fuskanta bayan ya aika File na shari'arta zuwa ofishin DPP na jihar Lagos domin samun shawara.

  Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

  Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Budurwa ta debo ruwan dafa kanta bayan ta yanke makogoron wata budurwa yayin fada Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });