An sace wani babban dan kasuwa a garin Zauro na jihar Kebbi

Wasu yan bindiga sun sace wani dan kasuwa mai suna Alhaji Murtala Zauro a gidansa da ke kauyen Zauro kusa da garin Birnin kebbi a jihar Kebbi ranar Asabar da dare bayan Sallar Isha'i'

Majiyarmu ta ce wasu mutane ne cikin dare suka aika wani dan karamin yaro cewa ya sallamo Murtala daga gidansa, fitowarsa ke da wuya sai suka tilasta shi ya shiga motarsu kuma suka arce da shi. Babu wanda ya san wajen da mutanen suka tafi da shi.

Kakakin yansandan jihar Kebbi DSP Danjuma Possi ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce yansanda na kokari kan lamarin, kuma kawo yanzu wayar Murtala tana kashe, hakazalika ba wanda ya tuntube iyalinsa ko yansanda dangane da wata bukata a kan lamarin kawo yanzu.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN