• Labaran yau

  An kama mai koyar da motsa jiki yana zina da wata matar aure a dakin koyon motsa jiki.Hotuna

  A yau, jakar magori ta samo mana labari ne daga kasar Zambia na wani mai koyar da motsa jiki a dakin motsa jiki a kasar Zambia da ya sha mugun duka, kuma aka tozarta shi bayan wani mutum mai suna Mr. Eugene Dsouza ya kama shi turmi tabarya yana lalata da matarshi Malama Dsouza da rana kiri kiri.

  Da farko dai Mr. Eugene shi da kanshi ne ya kai matarsa wajen motsa jiki domin a dinga koya mata yadda zata dinga motsa jikinta. Amma kash!....shi kam mai motsa jiki sai ya wuce lissafi, domin dai matar Mr. Eugene ta shiga soyayya da mai koya mata motsa jiki.

  Sannu a hankali fa lamari ya yi nisa, sakamakon haka ta fara nuna wasu halaye da maigida bai saba gani tana aikatawa ba. Sakamakon haka ya fara tuhumar kilan akwai lauje a cikin nadi.

  Daga bisani dai Mr.Eugene ya fara lallabawa domin ya gano ko miye ke faruwa, amma bayan ya kai ziyarar bazata a wajen motsa jiki kuma ba daidai lokacin da aka saba daukar darasi na motsa jiki ba, ai sai Mr.Eugene ya ga wani darasi ne daban mai koyar da jiki yake koya wa matarsa, domin dai Mr Eugene ya kama mai koyar da motsa jiki ne turmi tabarya yana sukuwan jima'i da matarsa tsirara.

  Nan take ya rufe shi da duka kuma ya dauki bidiyon tsiraicin matarsa da mai koyar da ita motsa jiki a yayin da suke neman afuwa. Wannan rigima ya jawo hankalin makwabta suka kawo dauki, amma sai suka tarar da abin da wannan mata da mai koya mata motsa jiki suka aikata.Daga bisani kuma Mr Eugene ya tura hoton bidiyon a shafukan sada zumunta domin ya tozarta matarsa da ya kira mazinaciya tare da mai koyar da motsa jiki.

  Mai koyar da motsa jiki ya tabbatar wa mijin matar watau Mr Eugene yayin da ake masa tambayoyi cewa shi kam ya dandana tsiraicin wannan mata ne har sau hudu, kuma ita ke kawo kanta , duk da yake baya so amma daga bisani dai sha'awarta ya rinjaye shi sai kuma suka fara aikatawa.


  Shiga shafin mu na Facebook facebook.com/isyakuweb

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0

  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

  Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kama mai koyar da motsa jiki yana zina da wata matar aure a dakin koyon motsa jiki.Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });