Abun kunya: Kalli yadda ‘Yan takarar APC suka bawa hammata iska a Zamfara


Sabani kan hanyar da za ai amfani da ita wajen fitar da ‘yan takara a jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya kai ga bawa hammata iska tsakanin ‘yan takara. Rikicin ya afku ne bayan an gaza cimma daidaito a kan tsarin da a ai amfani das hi wajen fitar da ‘yan takarar a jam’iyyar APC.

Tun da fari sai da kwamitin tsara zaben da uwar jam’iyyar APC ta turo ya fitar da tsarin da za a yi amfani da shi don gudanar da zaben, amma sai bangare na ‘yan takarar suka nuna rashin gamsuwa da tsarin, lamarin ya jawo barkewar cece-kuce da musayar yawu da ta kai ga har an bawa hammata iska.

Kwamitin zaben ya amince da gudanar da zaben ne ta hanyar kai tsaye, da ake kira kato bayan kato, amma sai bangaren masu adawa da dan takarar da gwamna Yari ya tsayar suka bayyana shakku a kan sharudan da kwamitin ya zayyana za ai amfani da su kafin gudanar da zaben.

Shi dai kwamitin ya gindaya sharadin cewar sai an tabbatar da sunan mutum a rajistar jam’iyya kafin a amince ya bi layi domin kidaya shi sannan sun nemi a kawo masu wasu ma’aikata daban da zasu gudanar da aikin zaben.

Wadannan sharuda ne bangaren masu adawa da dan takarar gwamna suka ce sam basu amince da su ba, su na masu nuna shakku a kan gaskiyar rajistar ‘yan jam’iyya da kwamitin ke shirin amfani da ita.

Tuni dai wasu masu nazarin siyasa ke jin tsoron cewar APC zata iya rasa dan takarar gwamna a jihar Zamfara, musamman ganin cewar yau ne hukumar zabe ta tsayar a matsayin rana ta karshe da zata karbi sunayen ‘yan takara daga jam’iyyu.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Hausa.naija.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN