2019: Marawa Atiku baya, barin PDP da sauran abubuwan da Kwankwaso zai iya yi a siyasa


Kun samu labari cewa Atiku Abubakar ne ya lashe zaben fitar da gwani na Jam’iyyar PDP inda ya doke irin su tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Kwankwaso. Kwanaki ne dai Kwankwaso ya fice daga APC ya koma Jam’iyyar PDP. Yanzu dai mun kawo maku manyan matakan da Kwankwaso zai iya dauka a Jam’iyyar PDP yayin da aka dunfari zaben 2019.

1. Takarar Sanata Yanzu dai Rabiu Kwankwaso yana iya neman komawa Majalisar Dattawa inda yake wakiltar Kano ta tsakiya. PDP dai ta tsaida Hon. Aliyu Madakin Gini a matsayin wanda zai nemi kujerar Sanatan sai dai yana iya maye gurbin sa kafin zaben 2019.

2. Marawa Atiku baya Haka kuma Sanata Rabiu Kwankwaso yana iya marawa Atiku Abubakar wanda ya samu tikitin PDP baya ya samu nasara a zaben 2019. Idan Atiku yayi nasara dai Kwankwaso na iya samun wani babban matsayi a cikin Gwamnatin sa. 3. Sauya-sheka Abin da kuma ya ragewa Sanatan shi ne ya koma Jam’iyyar APC ko wata Jam’iyya bayan 2019 bayan an tika sa da kasa a 2019.

Wasu dai su na ganin tuni tsohon Gwamnan na Kano ya lalata rawar sa da tsalle da ya bar Jam’iyyar APC. Jiya ne ku ka ji cewa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma Mataimakin sa Namadi Sambo hakurin abubuwan da ya faru tsakanin su a 2015.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Hausa.naija.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN