Zaben Osun: APC ta yi galaba a kananan hukumomi 3 cikin 4


Gboyega Oyetola, dan takarar gwamnan jihar Osun karkashin jam'iyyar APC a zaben ranar Alhamis da ake kan gudanarwa zagaye na biyu, ya baiwa takwaransa na jam'iyyar PDP Sanata Ademola Adeleke tazara mai nisa, inda ya lashe kuri'un kananan hukumomi 4 cikin 3 da ake gudanar da zaben.

Oyetola ya samu nasara a akwatuna biyu da ke Ile Ife ta Kudu, inda ya samu kuri'u 283, yayinda Ademola Adeleke, ya samu kuri'u 15. 

A karamar hukumar Ife ta Arewa kuwa APC ta samu kuri'u 126, yayin da Adeleke ya tashi da kuri'u biyu kacal. 

A dukkanin akwatunan zaben, an nemi jami'an sa ido na jam'iyyar PDP an rasa su ko sama ko kasa. Sakamakon zaben gunduma ta 5 a akwati na 7 na garin Alekuwodo da ke karamar hukumar Osogbo, APC ta samu kuri'u 299 yayinda PDP ta tashi da 165. 

Dan takarar kujerar gwamnan karkashin PDP, ya samu nasarar zuwa zaben zagaye na biyu da kuri'u 353 akan APC, sai dai daga alamu reshe ya juye da mujiya, don kuwa APC ta baiwa PDP tazara mai nisan gaske a kananan hukumomin 3 cikin 4 da ake gudanar da zaben. Ana gudanar da zaben raba gardamar ne a mazabu 7 dake kananan hukumomin jihar Osun 4. Ga jerin sakamakon kamar yadda suke a mazabun da aka gudanar da zaben

Orolu, mazaba ta 8, akwatu ta 4
APC 198 PDP 15
Orolu, mazaba ta 9, akwatu 3
PDP 64 APC 41
Karamar hukumar Ife ta kudu,
 akwatu ta 012
Adadin masu kada kuri’a da aka tantance 310
Kuri’ar da ta lalace 6
APC 283
APA 3
APGA 1
PDP 15
SDP 1
UPN 1
Mazaba ta 10, akwatu ta 02, karamar hukumar Ife ta arewa
APC 126
PDP 2
Mazaba ta 8, akwatu ta 10, karamar hukumar Ife ta kudu
APC 172
PDP 21
Mazaba ta 5, akwatu ta 17, karamar hukumar Osogbo
APC 299
PDP 165
Ife ta Arewa
APC 132
PDP 02
Zamu cigaba da kawo karin sakamkon zaben da zarar sun shigo hannu
 


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naija.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN