• Labaran yau

  Yadda wasu matan aure suka yi wa juna zindir akan saurayi

  Dambe ya kaure tsakanin wasu matan aure guda biyu sakamakon kishi a kan wani saurayi da suke soyayya da shi mai suna Chiemeziem a garin Okpoko, na karamar hukumar Ogbaru a jihar Anambra, lamari da ya kai ga yi wa junansu zindir a baiyanar jama'a.

  Bayanai sun nuna cewa matan wanda daya ma'aikaciyar gwamnati ce ita dayar kuma yar kasuwa ce, sun sha tayar da jijiyoyin wuya akan ko wacece ke da ikon mallakar soyayyar wannan dan talikin Chiemeziem.

  The Nation ta ruwaito cewa, tun ba yau ba, sun sha yi wa juna kashedi a kan mallakar Chiemeziem. Sakamakon haka, saurayin ya yi masu rosta, watau ya raba masu kwanaki da kowace za ta zo wajenshi. Ana cikin haka ne sai wata rana ita ma'aikaciyar gwamnati ta zo wajen saurayin a ranar da 'yar kasuwa take holewa da saurayin.

  Sakamakon haka aka sami zafafar musayar yawu da ya rikide zuwa damben kece raini a kan mallakar saurayi dan kabilar Igbo, wanda sakamakon haka fa aka kwashi yankallo, domin dai wadannan matan aure sun nishadantar da ajama'a da ke kewaye da su ne, bayan sun yi wa junansu zindir a bainar jama'a.

  Bayan an yi duk iya abinda za a iya yi domin a warware wannan fadar kuma lamarin ya gagara, sai saurayi ya turo dukkannin matan waje cikin fushi kuma ya kulle gidansa ya saka makulli a aljihu ya tafi abinsa.

  Bayanai sun ce dukannin matan sun haifar ma saurayin da ko diya kafi wannan lokaci.

  Tap, cakwakiya kenan, miye ra'ayin ka akan irin wannan makauniyar soyayyar ? rubuta ra'ayinka a wajen da ka gan Facebook comment a kasan wannan labari.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda wasu matan aure suka yi wa juna zindir akan saurayi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });