Mun samu labari cewa
Sanata Kabiru Gaya ya ji kunya wajen wani taro na Jam’iyyar APC mai
mulki da aka yi kwanaki inda aka karbi tsohon Gwamna Malam Ibrahim
Shekarau daga PDP zuwa APC a Kano.
A makon da ya wuce ne tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya fice
daga Jam’iyyar PDP ya dawo Jam’iyyar APC. A dalilin haka ne Shugaban
Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshimhole da wasu manyan Jam'iyyar su ka je
gidan tsohon Gwamnan.
Kamar yadda labari ya zo mana, manyan ‘Yan siyasar Kano su na wajen
wannan taro da aka yi. Sanatocin Jihar irin su Barau Jibril da Kabiru
Gaya da kuma wasu ‘Yan Majalisa sun halarci zaman da aka yi da tsohon
Gwamna Shekarau da sauya sheka.
A lokacin da ake gabatar da ‘Yan siyasar na APC, jama’a sun yi ta tafi
su na jinjina masu. Sai dai lokacin da aka zo kan Sanata Kabir Gaya
wanda ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, wasu sun yi masa ihu
har ta kai manyan APC sun sa baki a wurin.
Shugaban APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas sai da ya zagi wadanda su ka
yi wa babban Sanatan ihun ba su yi a wajen taron. Wasu sun nuna cewa ba
su tare da Sanatan inda su ke neman Jam’iyyar ta tsaida Kawu Sumaila a
matsayin Sanatan Kudancin Kano.
Kun samu labari cewa yayin da tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau
ya fice daga Jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki, Shugabannin Jam’iyyar
PDP da wasu manyan ‘Yan siyasar Kano sun nuna goyon-bayan su ga Sanata
Rabiu Musa Kwankwaso.
Jama'a su na yi wa Kabiru Gaya ihu a gaban Gwamna Ganduje da sauran
manyan Jam'iyya Read more: https://hausa.naija.ng/1191394-sanata-kabiru-gaya-ya-sha-ihu-a-gaban-manyan-apc-bidiyo.html#1191394Mun samu labari cewa Sanata Kabiru Gaya ya ji kunya wajen
wani taro na Jam’iyyar APC mai mulki da aka yi kwanaki inda aka karbi tsohon
Gwamna Malam Ibrahim Shekarau daga PDP zuwa APC a Kano.
Mun samu labari cewa Sanata Kabiru Gaya ya ji kunya wajen
wani taro na Jam’iyyar APC mai mulki da aka yi kwanaki inda aka karbi tsohon
Gwamna Malam Ibrahim Shekarau daga PDP zuwa APC a Kano.
A makon da ya wuce ne
tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga Jam’iyyar PDP ya dawo
Jam’iyyar APC. A dalilin haka ne Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshimhole
da wasu manyan Jam'iyyar su ka je gidan tsohon Gwamnan.
Kamar yadda labari ya zo mana, manyan ‘Yan siyasar Kano su
na wajen wannan taro da aka yi. Sanatocin Jihar irin su Barau Jibril da Kabiru
Gaya da kuma wasu ‘Yan Majalisa sun halarci zaman da aka yi da tsohon Gwamna
Shekarau da sauya sheka. A lokacin da ake gabatar da ‘Yan siyasar na APC,
jama’a sun yi ta tafi su na jinjina masu.
Sai dai lokacin da aka zo kan Sanata Kabir Gaya wanda ke
wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, wasu sun yi masa ihu har ta kai
manyan APC sun sa baki a wurin. Shugaban APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas sai
da ya zagi wadanda su ka yi wa babban Sanatan ihun ba su yi a wajen taron. Wasu
sun nuna cewa ba su tare da Sanatan inda su ke neman Jam’iyyar ta tsaida Kawu
Sumaila a matsayin Sanatan Kudancin Kano.
Kun samu labari cewa yayin da tsohon Gwamnan Kano Malam
Ibrahim Shekarau ya fice daga Jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki, Shugabannin
Jam’iyyar PDP da wasu manyan ‘Yan siyasar Kano sun nuna goyon-bayan su ga
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Jama'a su na yi wa Kabiru Gaya ihu a gaban Gwamna
Ganduje da sauran manyan Jam'iyya
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng