• Labaran yau

  Tashin hankali tsakanin Hausawa da yan kungiyar asiri, mutum 2 sun mutu

  An sami barkewar hargitsi sakamakon wani fada da ya tashi tsakanin wasu al'umman Hausawa yan kasuwa da wasu yan kungiyar asiri a rukunin gidajen Cable Point Quarters da ke Asaba a jihar Delta ranar Talata.

  Majiyarmu ta ce rikicin ya barke ne bayan yan kungiyar asirin sun kaima Hausawa hari bisa wasu dalilai na kashin kansu. Kuma yayin gudanar da aikin kwantar da hargitsi, wasu jami'an yansanda sun sami raunuka yayin da ake fargaba cewa yan kungiyar asiri biyu sun sheka Barzahu a rikicin.

  Wata majiya ta ce lamarin ya faru bayan gardama ta kaure tsakanin wani dan kungiyar asiri da wani Bahaushe kan cinikin Zinari da wasu kudaden kasar waje na Dala.

  Sakamakon haka yan kungiyar asirin suka daba ma wasu Hausawa wuka a hannu, yanayi da aya haifar da tsananin zubar jini, sakamakon haka ya sa sauran Hausawa suka yi gangami domin daukar fansa da kare kansu.

  Kwamishinan yansanda na jihar Mustapha Muhammed, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce rundunarsa ta kama mutum shida dangane da wannan rikici.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tashin hankali tsakanin Hausawa da yan kungiyar asiri, mutum 2 sun mutu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });