Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, jam'iyyar
adawa ta PDP ta bayyana cewa, a kullum kudiri gami da sa ran da kuma fatan
shugaban kasa Muhammadu Buhari na samun nasara a zaben 2019 kara disashewa
yake.
Jam'iyyar ta ke cewa,
dukkanin alamu na zamantakewa, tattalin arziki da kuma siyasa sun tabbatar da
cewa nasarar shugaba Buhari a zaben 2019 na ci gaba da disashewa sakamakon
ababe na datse kwararar romon dimokuradiyyar a kasar nan daga bangaren fadarsa
da kuma jam'iyyar APC.
Jam'iyyar cikin lasar tsinin takobi ta bayyana cewa, muddin
aka tafi akan haka to kuwa sai ta ga bayan shugaba Buhari kan kudirin da ya
sanya a gaba na neman tazarce a zaben 2019. Cikin wata sanarwa a ranar Alhamis
din da ta gabata da sanadin kakakin jam'iyyar, Mista Kola Ologbondiyan ya
bayyana cewa, rashin amincewa da sabuwar dokar zabe daga bangaren shugaba
Buhari ta tabbatar da cewar shi da jam'iyyar sa ta APC sun kidime wajen neman
duk wasu dabaru na gudanar da magudin zabe.
A sanadiyar haka kakakin jam'iyyar ke kira ga majalisar
dokoki ta tarayya, akan tayi gaggawar shigar da wannan doka cikin kundin tsari
na kasa ba tare da amincewar shugaba Buhari ba domin rusa duk wani shiri na sa
da jam'iyyar APC wajen gudanar da magudin zabe..A yayin haka kuma, jam'iyyar
tana zargin shugaba Buhari da bujoro da wata hanyar basaja gami da yaudarar
al'ummar kasar na wajen sayen fam din tsayawa takara na jam'iyyar APC akan
zunzurutun kudi na N45m.
Take cewa, an yi walkiya kuma shugaba Buhari ya bayyana a
gaban al'ummar kasar nan inda tuni suka dawo daga wannan rakiya ta sa ta afkawa
cikin duk wata yaudara da zai gabatar a gare su.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
Tags:
LABARI