• Labaran yau

  Neman yin suna ya sa wani mutum lullube jikinsa da kudan zuma

  Wani mutum dan kasar Saudiya ya sake yin yunkurin bajinta  domin ganin sunansa ya shiga littafin Guinness Book of Records da ke tattara ababen hazaka da bajinta da ban al'ajabi a doron Duniya. Zahair Fatani ya rufe jikinsa ne da kudan Zuma fiye da 20.000.

  Zahair ya shafe shekara 30 yana kula da kudan Zuma, kuma ya aikata haka ne domin ganin ya doke wanda ke rike da wannan darajar dan kasar China mai suna Ruan Liangming wanda sunansa ya sami shiga littafin sakamakon kasancewa mutumin da kudan Zuma masu nauyin 63.7kg (140 lb 6.95 oz) suka taba sauka a jikinsa, ciki har da Sarauniyar Zuma guda 60 masu ban tsoro.

  Yayin da Zahair ya yi yunkurin yin wannan harka a bara, wata Sarauniyar kudan Zuma ta tashi daga jikinsa ta yi tafiyarta, sakamakon haka dubban kudan Zuma maza suka tashi suka bi ta, lamari da ya sa harkar ta watse a bara. A bana kuma, Zahair ya sake auna sa'arsa.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Neman yin suna ya sa wani mutum lullube jikinsa da kudan zuma Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });