• Labaran yau

  Labarin yadda wata mata ta auri maza biyu

  Allah daya gari ban ban inji Malam Bahaushe, wata mata ce a kasar Kenya mai suna Rael Mukeku ta auri maza biyu a wani yanayi mai ban mamaki, Mukeku yar shekara 35 ce wacce ke da yara 11 kuma tana zaune a Tsaunukan gundumar Makueni a kasar ta Kenya.

  Wanan mata ta yi auren fari tun tana da shekara 10 a Duniya, yar Gogoro da tabar gari, Mukeku ta sami kanta a cikin wannan yanayi sakamakon talauci.

  Duk da yake ta daina halin shaye shaye da tabar gari, mijinta na farko Muema Nguu dan shekara 50 talakan gaske ne wanda baya da cikakken lafiya, kuma baya iya jima'i, sakamakon haka ya sa ala tilas ta yi tunanin wani aure daga Kauyen.

  Shi dai mijinta na biyu Mutuku Muia dan shekara 45 lebara ne, kuma abokin mijinta na farko, duk da yake an dan sami rashin amincewa daga mijinta na farko, amma ala tilas ya hakura daga karshe ganin cewa har abada ba zai iya jima'i da mace ba sakamakon rashin lafiya.
  Ita dai Mukeku ta haifa wa mijinta na biyu yaya, kuma ana zaune a cikin irin wannan yanayi yanzu haka. Amma mijinta na biyu yakan zo wajenta ne akalla sau biyu kacal a wata daya, yayinda mijinta na farko yana tare da ita a gida daya kullum.
  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Labarin yadda wata mata ta auri maza biyu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });