Ko 'yan Social Media 'yan Jarida ne ?

Isyaku.com | 29-9-2018 |

Najeriya ta bi sahun sauran  kasashen Duniya wajen cin gajiyar gagarumin aikin da massanan suka yi na kirkiro shafukan sada zumunta, wanda Biliyoyin jama'a ke amfana da shi a Duniya. Amma fa akwai wata matsala daya da ta addabi jama'ar Najeriya wanda haka ya sha kawo rudani ko shin masu amfani da kafar Facebook suna aika labarai wannan yana nufin su yan Jarida ne kenan?.

A yawancin jihohin Arewacin Najeriya, hatta wasu Gwamnoni kan yi amfani da kafar Facebook wajen fitar da muhimmin bayanan Gwamnati kafin wadannan bayanai su fara fitowa daga kafofin watsa laabarai mallakar ita kanta Gwamnatin wadannan jihohin. Sakamakon haka aka haifar da rashin tsari mai inganci wajen tafiyar da watsa labarai ga al'umma kuma daga bisani ya zama barazana ga mutunci,daraja,muruba da kuma nagartar gidajen Jaridu tare da martabar aikin Jarida.

Binciken mu, kuma kamar yadda jama'a suka sani ne, ya nuna cewa, mafi yawan matasa da ke aika labarai daga Facebook basu yi karatun aikin Jarida ba, ko kuma basu yi wani Kwas, ko suka sami wani horo na musamman akan aikin Jarida ba. Akasarin wadannan samari sukan dauki wayar salularsu ce su dauki hotuna kuma su aika tare rubutu da suke so. Mai amfani da Social media shi ne wanda ke iyartar shafin Facebook,Whatsapp ko Twitter da sauransu domin sada zumunta bisa ka'ida. Dan Social Media kuma shi ne mai aikin sa kai, watau Dan Agaji na Social media wanda ke neman suna, kulawa ko wata bukata ta hanyar kwasa zuba, ko rubuce-rubuce bisa wata manufa, ko domin ya ci ma wata biyan bukata ta hanyar jawo hankalin jama'a zuwa gareshi.

Wasu daga cikin irin wadannan matasa kuma sukan kwaikwayi salon rubutun yan Jarida, da salon gabatarwa sai suyi rubutu su aika wa abokai . Har ma wani sa'ili sukan kira kansu 'yan Jarida. Amma bincike da muka gudanar ya nuna cewa duk da yake su kansu wadannan matasa sun san su ba yan Jarida bane, amma rinjayensu basu iya dukawa yan Jaridan na ainihi balle a taimaka masu da horo domin su inganta abin da suke yi.

Wani masani kan harkar ingizon yanar gizo da sadarwar zamani Dr.Emmanuel Peters Adeleke, yace, " mafi yawan wadanda ke rubutu suna turawa a shafukan Facebook da sunan su yan Jarida ne alhali basu yi karatun aikin Jarida, ko suka sami horo na musamman akan aikin Jarida ba, mutane ne da idan ka lura za ka gan cewa mutane ne masu son nuna isa, fice, ko masu karambanin gaske a cikin al'umma".

Dr Adeleka ya kara da cewa" babu wanda ya isa ya ce shi Likita ne, ko Injiniya ko wani kwararre a kan wani fannin Ilimi ba tare da asirinsa ya tonu ba, amma sai kowa ya yi ma aikin Jarida hawan kawara, kuma ba tare da an dauki wani mataki ba domin yanzu jama'a sun fi yarda da rashin gaskiya  matukar suna ganin za su sami wani sauki ta haka, sai su rungumi gurguwar tsari marmakin ingantaccen tsari:.

Daga lokacin da mai amfani da Facebook ya aika labari, ba wai yana nufin ya yi aikin Jarida bane ko da ya yi rubutu irin na jarida, domin aikin Jarida ko da cikakken dan Jarida ne kai,kana bukatar gidan Jaridar ita kanta, shafin Jaridar a zahiri ko a yanar gizo, adireshin shafin Jaridar na yanar gizo domin jama'a su ziyarta, sai kuma dole ne ya kasance wanda ya rubuta labari akwai sunansa a kan kowane labari. Hakazalika bayan an wallafa labarai a uwar shafin jarida, daga bisaani akan tura zuwa kafoin sada zumunta kamarsu Facebook,Twitter,Instagram, Youtube da sauransu na wannan shafin Jarida.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN