Type Here to Get Search Results !

Kasar India ta halatta yin luwadi da madigo


Rahotanni sun kawo cewa kotun koli a kasar India ta halasta yin luwadi da madigo a kasar, matakin da aka dade wasu na adawa da shi. Kotun ta halatta yin hakan ne ga manya da suka mallaki shekarun girma.

 Hukuncin dai ya yi wa masu gwagwarmayar kare 'yan luwadi da madigo dadi inda suka rungume juna suna murna bayan yanke hukunci da kotun tayi. Alkalai biyar ne suka yi nazari akan hukuncin da aka yanke a shekara ta 2013.

Tsohuwar dokar tun zamanin turawan mulkin mallaka da aka fi sani da sashe na 3-7-7 ta zartar da hukuncin duk wanda aka samu da yin madigo da luwadi za a yanke masa hukuncin ko dai sama da shekara 10 a gidan kurkuku.

Tun da farko ma su fafutuka sun ce ayyana auren jinsi a matsayin laifi, zai zama babbar barazana ga 'yancin masu ra'ayin auren jinisi daya. A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Allah madaukakin sarki ya tona asirin wani hamshakin dan kasuwan jihar Kano da ya shahara wajen aikata luwadi da kananan Yara.

 Majiyarmu ta ruwaito a ranar Laraba 25 ga watan Yuli ne wata Kotun majistri dake jihar Kano ta aika da wannan attajiri, Balarabe Habibu zuwa gidan Yari sakamakon zarginsa da ake yi da yin luwadi da wani yaro mai shekara Tara.

Dansanda mai shigar da kara, Sufeta Pogu Lale ya shaida ma Kotun cewa Habibu mai shekaru 41 mazauni a unguwar Dullurawa ya aikata luwadi, wanda hakan ya saba ma sashi na 284 na kundin hukunta manyan laifuka.

Dansandan yace mahaifin wannan yaro mai suna Muratala Sa’idu tare da mahaifiyarsa Aisha Khalid ne suka kai karar wannan mutumi zuwa ofishin Yansanda dake Jakara a ranar 6 ga watan Yuli.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN