Duk da cewa kasar Najeriya ba mai yawan samun mummunar
girgizan kasa bace kamar sauran sassan kasashen Duniya, amma anan gida Najeriya
akan samu wasu yan kananan girgizan kasa, wand aka iya sanya mutane cikin
firgici da rudani.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito tun daga ranar Laraba har zuwa
Juma’a 7 ga watan Satumba anyi ta samun karamin girgizan kasa a babban birnin
tarayya Abuja, wanda hakan ya firgita mazauna unguwannin Mpape da Maitama
sakamakon wannan ne karo na farko da suka fuskanci lamarin.
Sai dai baya da Abuja, an taba samun kwatankwacin wannan
girgizan kasar a jihohin Kaduna, Ogun, Bayelsa, Ribas da Oyo, kuma bincike ya
nuna irin wannan girgizan na farko a Najeriya ya faru ne a shekarar 1933.
Rahotanni sun bayyana cewa kasar China ce kasar dake kan gaba wajen samun
girgizan kasa, inda a jimlace girgizan kasa ya kashe sama da mutane dubu dari
takwas (800,000) a kasar tun daga shekarar 1900 zuwa 2016.
Haka zalika bincike ya nuna abubuwan dake janyo irin wannan
karamin girgizan sune matsawar wasu sinadarai a karkashin kasa, haka zalika
ayyukan mutane kamar su fasa duwatsu da nakiya, hakar man fetir, hakar
ma’adanan kasa da kuma fashewa makamin nukiliya na iya kawo girgizan.
Sai dai fa binciken yace babu abinda zai iya hana faruwar
wannan girgizan, sai dai kawai kwararru a harkar gine gine su dinga kulawa
wajen gine gine saboda gidaje ne lomar farko idan lamarin ya faru, amma akwai
wasu hanyoyi bakwai da ka iya tseratar da mutum idan girgizan ya faru;
- Kada a firgita, ka natsu ka nemi wajen tsira
- A kashe na’urar iskar gas, da kayan wuta don hana gobara
- A kauce ma wayoyin wutar lantarki, bishiyu da gadoji
- Idan ana cikin daki ne na kwanta da hannuwanka a bayan
kanka ka shige karkashin tebur
- A kauce ma dakin girke girke da tagogi don kada girgizan
ya jefo maka wuka ko gilashi
- A ajiye wayar salula a kusa a kira lambobin bada agajin
gaggawa
- A nemo akwatin magunguna a ajiye a kusa saboda kota kwana
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng