Type Here to Get Search Results !

Main event

Jami'an FRSC 2 sun sha duka a hannun wasu fusatattun jama'a - Bidiyo

Wasu jami'an hukumar FRSC a jihar Anambra sun gamu da wulakanci a hannun wasu fusatattun jama'a bayan an yi zargin cewa jami'an FRSC ne suka haddasa wani hadari da ya yi sanadin rauni ga fasinjojin wasu motoci guda biyu da suka yi hadari ciki har da wata mace mai juna biyu.

Majiyarmu ta ce jami'an FRSC din da ke gudanar da aikin sintiri, sun biyo wata mota ce a guje, sakamakon haka kuma aka yi taho mu gama da wata motar fasinja, lamari da ya haifar da wannan hadari.

Fusatattun jama'a da ke wurin sun kama wasu jami'ai na FRSC guda biyu da ke gudanar da sintirin, kuma suka wulakanta su a bainar jama'a, har da tilasta su zama a kasa bayan sun sha duka.

Daga karshe wani jami'in dansanda ya zo ya kuma ya nemi jama'a su daina dukan jami'an na FRSC. An garzaya Asibiti da wadanda suka sami raunuka.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies