• Labaran yau

  Hotunan hadarin mota da ya rutsa da Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello

  Bayan karyata rahoton cewa ayarin motocin Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello sun sami hadari a kan hanyarsu ta zuwa Abuja ranar  Litinin, wanda mai taimaka wa Gwamna Yahaya Bello kan harkokin watsa labarai Kingsley Fanwo ya yi, sai ga wasu hotuna sun bayyana wadanda ke tabbatar da faruwar lamarin.

  Majiyarmu ta ce hadarin ya faru a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja, watau a kan hanyar filin saukar jiragen sama na Abuja. Majiyar ta ce hadarin ya faru a kan Gadar Jamata da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja bayan wani dan acaba ya kawo rudani a ayarin motocin Gwamnan yayin da suke tafiya.

  Yayin kaucewa dan acaban sai motoci biyar suka dinga kauran jina kuma sakamakon haka wadansu motocin suka stunduma a gwata da ke gefen titi.

  Rahotanni sun ce mutum biyu a cikin ayarin Gwamnan da mutum biyu da ke kan acaban sun sami raunuka kuma an garzaya da su Asibiti domin karbar magani.

  Gwamna Yahaya Bello dai wani masoyin shugaba Buhari ne kuma yana kan hanyarsa ce ta zuwa fadar shugaban kasa domin ganawa da shugaba Buhari dangane da matsalolin ambaliyar ruwa da ya rutsa da jiharsa.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotunan hadarin mota da ya rutsa da Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });