Dalilai 3 da ka iya sa Shugaba Buhari shan kasa a zaben 2019


Yayin da zabukan gama-gari na shekarar 2019 ke kara matsowa, kusan a iya cewa duk wani dan siyasa yanzu hankalin sa ya karkata ne a can bangaren.Kamar dai yadda aka zata, masana harkokin siyasa da masu sharhi akan al'amurran yau da kullum a ko da yaushe sukan dauki lokaci suna bincike sannan kuma su bayyanawa jama'a yadda suke hasashen zabukan za su kasance.

NAIJ.com ma a nan ta danyi bincike akan wasu dalilan da ka iya sa shugaba Muhammadu Buhari ya fadi zaben 2019 idan har ba'a yi gyara ba.

1. Rashin adalci wajen nade-naden mukamai Masu sharhi akan al'amurran siyasa a kasar nan dai na ganin dole ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake yin duba akan yadd yake yin nade-naden sa saboda al'ummar kudancin kasar na zargin ba yayi masu adalci. Duk da dai shugaban kasar ya sha karyata hakan.

2. Yiwuwar sasanci a tsakanin 'yan takarar adawa Haka ma dai ana ganin idan har 'yan adawa musamman ma na jam'iyyar PDP dake neman tikitin yin takarar da Shugaba Buhari a 2019 suka hada kan su suka fitar da mutum daya kwakkwara, to lallai za su iya kayar da shi.

3. Rarrabuwar kuri'un yankin Arewa Kowa yasan da yawa daga magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari, duk daga yankin arewacin kasar nan suke. To ana ganin idan har jam'iyyun adawa suka raba kawunan 'yan arewar musamman ma wajen kuri'un su, to tabbas za su iya kada shi a zaben.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naij.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN