Zaku ji cewa tsananin adawa dake tattare cikin siyasa
musamman ta kasar nan ta sanya gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya fatattaki
hadiman gwamnatin sa kimanin 28 kamar yadda rahotanni da sanadin shafin jaridar
The Nation suka bayyana. Rahotannin sun bayyana cewa, gwamnan ya sallami
hadiman sa na musamman guda 17, yayin ya yiwa manyan hadiman sa 11 sallama ta
'Umma ta gaida Assha' cikin ruwan sanyi domin yiwa gwamnatin sa garambawul da
sauya fasalin 'yan majalisa da makarrabansa.
Sakataren gwamnatin jihar, Tony Ijoho, shine ya bayar da
sanarwa yanke alakar hadiman 28 da kuma gwamnan jihar, inda ya neme su akan
mika dukkanin wani mallaki na gwamnatin a hannun sakatarorin su na dindindin.
Binciken manema labarai ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta raba gari da
hadimanta ne domin bai wa sabbi dama ta maye guraben su musamman 'yan jam'iyyar
adawa ta PDP.
NAIJ.com ta fahimci cewa, gwamna Ortom ya karbi ragamar
gudanar da al'ummar jam'iyyar PDP tun yayin da ya sauya sheka ta ficewa daga
jam'iyyar APC. Gwamnan yana daya daga cikin jiga-jigan kasar nan da guguwar
sauyin sheka ta kada su yayin da suka yi hannun riga da jam'iyyar ta APC
makonni kadan da suka gabata.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng