Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma dan takarar shugaban kasar
Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi ma
jam’iyyar PDP barazana game da yawan magoya bayansa dake yankin Arewacin
Najeriya, da aka fi sani da ‘Yan KwankwasiyyaMajiyar NAIJ.com ta ruwaito
Kwankwaso yayi wannan baki ne a yayin daya yanki takardar takarar shugaban kasa
a babban ofishin jam’iyyar PDP, inda yace akwai dan Kwankwasiyya a kowanne gida
dake Arewacin Najeriya, karanci kenan.
“Mun yi aiki tukuru muka samar da tafiyar Kwankwasiyya, ina
fada maka a yau abin mamaki ne ace an samu gidan da babu dan Kwankwasiyya a
kafatanin yankin Arewa gaba daya kwata, ya kamata a sani cewa yayan
Kwankwasiyya suna da da’a, ladabi da biyayya, kuma muna da burin gyara
Najeriya.
“Na tabbata kaga
Kwankwasawan da suka halarci taron kaddamar da takarata, inda matasa maza da
mata suka daga dukkanin sassan Arewa suka fito, wasu ma motar Tirela suka bi,
duk da cewa ana damuna, amma basu damu ba, ko a jikinsu.
“Murna ma suke yi, saboda bukatarsu a samu kyakkyawan
shugabanci a Najeriya, kuma nima ina farin cikin samun jajirtattun matasa
kamarsu suna mara min baya, ba kudi suke nema ba, mutane ne da suke da burin
ganin sun kada kuri’u, kuma sun kare kuri’unsu, wannan shine ma’anar
Kwankwasiyya, kuma da wannan nafi karfin sauran masu takarar shugaban kasa a
PDP.
” Inji shi. Jam’iyyar PDP ta sanar da fara sayar da takardar
takarar shugabancin kasar nan ga masu sha’awar yin haka daga cikin yayanta,
inda ta sanya shi akan kudi naira miliyan goma sha biyu.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng