Kebbi: APC da PDP na tantance wakilai zaben fid da gwani, dan Bagudu ne APC ta tsayar

Aikin tantance Wakilai wadanda za su kada kuri'a a zaben fitar da gwani na mukamin Gwamnan jihar Kebbi ya yi kusan kammala. Jam'iyyun APC da PDP suna gudanar da tantancewar ne a wurare daban daban a cikin garin Birnin kebbi. Akwai wadatattun jami'an tsaro a dukannin wuraren da ake gudanar da wannan aiki domin tabbatar da lafiyar jama'a da ganin cewa an kammala aikin lafiya.

Jam'iyyar APC tana gudanar da tantancewar a Makarantar Pramare na Kauran Gwandu da ke Makerar Gandu, ita PDP tana gudanar da  nata a garin Gwadangaji.

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kebbi Arch.Bala Sani Kangiwa, ya shaida mana cewa "Gwamna Atiku Bagudu ne kadai dan takara tilau da Jam'iyyar APC ta tsayar".

Bayananin shugaban jam'iyyar APC ya kawar da jita-jita da ke zagayawa har da rudani kan lissafin nazari ga jama'a ko miye sahihin matsayin dan takarar kujerar Gwamna a jam'iyyar APC Alh. Ibrahim Mera Chiroman Kabbi kan wannan takara ta kujerar Gwamnan jihar Kebbi. Kuma wadannan kalamai na Arch.Bala Sani Kangiwa sun warware kunshin kayan Koli domin kowa ya gan abinda ya kunsa.

Yunkuri da muka yi domin samun Alh.Ibrahim Mera ta wayar Salula domin jin ta bakinsa a kan wannan lamari ya ci tura, domin dai bai amsa kiraye kiraye da muka yi masa ba kafin mu rubuta wannan rahotu.

Wata majiya ta rada mana cewa, nan da dan lokaci kadan bayan tantance Wakilai, za a je babban Filin wasa na Haliru Abdu, domin amincewa da Gwamna Atiku Bagudu a matsayin dan takara na jam'iyar APC a jihar Kebbi.

Daga Isyaku Garba

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN