Labarin da muke samu daga majiyoyin mu dai na nuni ne da
cewa babban jami'in sojan Najeriyar nan watau Manjo Janar Idris Alkali da muka
baku labarin bacewar sa a kwanan baya an tsinci gawar sa.
Mun samu cewa dai an
tsinci gawar sojan ne a garin Jos ta jihar Filato a kusa da asibitin koyarwa ta
jami'ar tarayya dake jihar akan hanyar zuwa matsugunnin jami'ar na din din din.
NAIJ.com dai ta samu cewa jami'an tsaron Najeriya ne suka gano gawar ta sa tare
da wasu masu sana'ar adai-daita a cikin wani kududdufi dake a garin.
Haka zalika dai majiyar tamu tace ana kyautata zaton 'yan
kabilar Birom ne dake a jihar suka kashe su duk da yake dai har yanzu ba samu
wani bayani ba daga hukumar sojin kasar game da lamarin. A wani labarin kuma,
Yayin da zabukan shekarar 2019 ke ta kara karatowa, wasu masoyan dan takarar
shugabancin kasar dake neman tikitin tsayawa a jam'iyyar adawa ta PDP, Dakta
Rabi'u Musa Kwankwaso sun yanka rago tare da addu'o'i ga Allah akan muradin na
su.
Kamar yadda muka samu, masoyan na Kwankwaso da galibin su
matasa ne sun fito ne daga karamar hukumar Kiru dake a jihar Kano inda kuma
suka gudanar da Sallah da saukar al'qur'ani duk domin samun nasarar gwanin
nasu.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naij.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI