Type Here to Get Search Results !

Main event

Abu Najakku ya mika Fom din takara a sakatariyar APC Kebbi na wakilcin B-kebbi,Kalgo,Bunza

Ali Bature Sakataren kudi,Arch Bala Kangiwa Chiyaman APC jihar Kebbi, Abu Najakku dan takara
Dan takaran kujerar dan Majalisar  tarayya mai wakiltar Birnin kebbi, Kalgo da Bunza, Comrade Abu Najakku, ranar Lahadi 9 ga watan Satumba 2018, ya mika takardarsa watau Form na neman takarar kujerar da yake nema ga uwar jam'iyar APC na jihar Kebbi da misalin karfe 12:00 na rana. Shugaban APC na jihar Kebbi Arch. Bala Sani Kangiwa da Mataimakinsa Alh. Abubakar Kana, Ali Bature, Sakataren kudi da sauran manyan jami'ai a jam'iyar na jihar Kebbi na cikin jerin manya da suka tarbi Abu Najakku a Sakatariyar jam'iyar da ke unguwar GRA a Birnin kebbi.

Shugaban yakin neman zabe na Abu Najakku, watau Comrade Bello Sani, ya fara da yin takaitaccen jawabi ga shugabanni da jama'a da ke Sakatariyar,  inda ya bayyana kyawawan halaye na Abu Najakku, da sukka hada da gaskiya, rikon amana, taimakon Al'umma da son ganin Talakawa sun sami cin gaba da samun sauki a rayuwarsu.

Abu Najakku na gaisawa da jama'a a Sakatariyar APC jihar Kebbi
Daga bisani Ab Najakku, ya kara haske dangane da asalinsa, Najakku ya bayyana hakikanin dalilai da suka sa ya shigo Siyasa, yace " Na shigo Siyasa ne bisa bukatar jama'a da suka neme ni in shigo domin in bayar da nawa gudunmuwa ta hanyar yi wa shugaba Buhari hidima, in yi ma Gwamna Atiku Bagudu hidima, in kuma yi ma jama'ar Birnin kebbi , Kalgo da Bunza hidima".

"Zan baku ingantaccen wakilci idan kun zabe ni domin in wakilceku a Majalisar Tarayya, lokaci ya yi da za ku bude ido domin ku zabi ingantaccen wakili da zai baku ingantaccen wakilci, Majalisa turanci ake yi, na kuma lakanci Turanci domin ni na yi koyarwa a Makaranta, na koyar da dimbin Dalibai Turanci har suka yi Digiri a harshen Turanci. Lokaci ya wuce da za ku zabi mutum ya yi ma rigarshi sitaci, illa karshen wata ya karbi albashi da alawus ya ci kudin tare da iyalinsa kawai.

Abu Najakku da wani abokinsa a Sakatariyar APC jihar Kebbi
Ku zabi wanda zai dinga waiwayan ku idan an zabe shi, ba wai wanda bayan kun zabe shi sai bayan shekara 3 zai sake zuwa wajenku domin neman kuri'arku ba".

A nashi jawabi, shugaban jam'iyar APC na jihar Kebbi, Arch Bala Sani Kangiwa, ya ce " Na sha ganin Kasidun Abu Najakku inda yake rubuce rubuce domin kare martabar Area da shugaba Buhari tun kafin in hadu da shi a yau. Kuma kamar yadda ya bukata , za mu yi wa duk yan takara adalci domin ganin bamu rasa kujerar mu ba ta hanyar shari'a".
Abu Najakku yana jinjina wa jama'a a Sakatariyar APC jihar Kebbi

"Domin dai idan Allah ya yarda, APC a jihar Kebbi za ta lashe zabe daga Mazabu har zuwa mataki na Tarayya, sakamakon haka yake da kyau mu sami yan takara da basu da wata matsala ko na takardu, ko martaba. Abokan hamayyar mu sun san bazasu sami nassara ba a kan mu, sakamakon haka za su yi amfani da inda muka yi kuskure domin su karbe kujerar mu ta hanyar shari'a, kuma bamu son haka ya faru".

Don haka ya zama wajibi mu yi bincike domin kauce wa rasa kujera ta hanyar shari'a, duk wani dan takara da muka gano yana da wata matsala, za mu bashi hakuri domin kada bayan an zabe shi, daga bisani a karbe mana kujerarsa ta hanyar shari'a. Za mu yi adalci ga duk yan takaran mu".
Abu Najakku bayan ya mika Fom dinsa, ya fito daga Sakatariyar APC na jihar Kebbi

Daga karshe, Comrade Abu Najakku ya fice daga cikin harabar jam'iyar ta APC yayiin da yake gaisawa da dandazon magoya bayansa.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies