Zan tsaya takaran Gwamnan jihar Kebbi 2019 a jam'iyar APC - Chiroman Kebbi Ibrahim Mera

Isyaku.com | 29-8-2018 |

Alh Ibrahim Mera, Chiroman Kebbi, ya kaddamar kuma ya bayyana aniyarsa na tsayawa takaran kujeran Gwamnan jihar Kebbi a zaben 2019 karkashin jam'iyar APC. Mera ya bayyana haka ne yayin da yake wa dimbin magoya bayansa bayani a ofishinsa na harkokin siyasa a Gwadangaji ranar Laraba.

Da misalin karfe 3:30 na rana ne Chiroman na Kebbin Argungu ya shiga garin Birnin kebbi kuma ya zarce kai tsaye zuwa gidan Mai martaba Sarkin Gwandu inda ya yi gaisuwan ban girma.

Daga bisani tawagarsa ta tafi ofishin jam'iyar APC na jihar Kebbi, amma wata majiya ta shaida mana cewa Sakataren kudi na jam'iyar APC na jihar Kebbi Ali Bature ne ya karbe shi domin shugaban jam'iyar yana Saudiya.

Amma tun da sanyin safiya, jami'an yansanda suka fara bayar da tsaro a Sakatariyar jam'iyar APC da ke gefen tsohon NITEL a unguwar GRA Birnin kebbi. Hakazalika, hatta matsaa da yan mata da aka saba gani a harabar Sakatariyar APC na jihar Kebbi sun yi batan dabo a yau, domin dai babu kowa face jami'an yansanda da ke bayar da tsaro.

Chiroma ya isa ofishinsa ne a jerin gwanon motoci zuwa garin Gwadangaji, inda ya yi jawabai, ya kuma nuna aniyarsa na tsayawa takaran kujerar Gwamnan jihar Kebbi a karkashin jam'iyar APC.

An ga Kwamishinan yansanda na jihar Kebbi CP. Ibrahim Kabiru a wajen taron , inda yake zagayawa domin tabbatar da tsaro. Hakazalika, Kakakin hukumar yansanda na jihar Kebbi DSP Suleiman Mustapha, ya shaida mana ta wayar salula cewa "Kwamishinan yansanda ya je wajen da kanshi domin tabbatar da tsaro, kuma jami'an mu suna wajen. Daga karshe dai an kammala wannan taro lafiya kalau".

Wadannan kalamai na Kakakin hukumar yansanda na jihar Kebbi, ya kawo karshen wata jita-jita da ya fara zagayawa cewa an yi sare sare har da fasa motoci biyu a garin Gwadangaji bayan an kammala taron.

Daga Isyaku Garba, Amina Muhammed da Ibrahim Manga

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN