• Labaran yau

  Wani magidanci ya tsere bayan ya banka wa masoyiyar sa da ‘ya’yanta biyu wuta


  Wani mutumin kasar Indiya, Jalil Khan, ya banka wa masoyiyarsa, Sangita Suresh Devre, tare da ‘ya’yanta biyu wuta, kamar yadda ‘yan sanda suka sanar a a yau, Litinin. Khan ya cinna wa Devre wuta ne tare da wata diyar ta dake da aure da kuma jariri saboda wani karamin sabani day a shiga tsakaninsu.

  A yayin da jaririn mai watanni 9 a duniya ya mutu, Devre da babbar yarinyar ta sun samu munanan raunuka sakamakon konewar da suka yi. Yanzu haka an kwantar da su a wani asibiti mai zaman kansa, Nashik Civil Hospital, inda aka bayyana yanayin da suke ciki a matsayin mai munin gaske, kamar yadda jami’in ‘yan sanda Madhukar Kad, ya sanar.

  Yanzu haka Khan ya cika wandonsa da iska tun bayan aika-aikar da ya yi. Khan da Derve sun shafe fiye da shekara daya suna cin holewa a matsayin masoya duk da cewar yana da aure. Sun samu sabani ne da ya kai su da yin muhawara mai zafi ranar Lahadi.

  ‘Yan sanda sun bayyana cewar Khan ya dawo gidan Devre da talatainin dare tare da kwara wa Devre da diyar tad a kuma jikanta kalanzir sannan ya cinna masu wuta. Har yanzu ana kokarin gano inda Khan ya shiga domin a kama shi.
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu 
  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  Hausa.naij.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani magidanci ya tsere bayan ya banka wa masoyiyar sa da ‘ya’yanta biyu wuta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });