• Labaran yau

  Tsohon biri dan shekara 42 ya lalata ýar makwabcinsa mai shekara 11


  Wata kotun majistare dake Ikeja ta gurfanar da wani mai aikin gini dan shekara 42 , Isaac Yakubu a kurkukun Kirikiri kan zargin lalata yarinyar makwabcinsa yar shekara 11 a duniya. Alkalin kotun P. E. Nwaka yace a cigaba da tsare Yakubu har zuwa lokacin da zai ji shawarar da daraktan sashin hukunta jama’a zain yanke. Yakubu, wadda ke zama a gida mai lamba 4, unguwar Mustapha Adeleke, Abule-Odu, Egbeda, ya aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Yuli a gidansa. Jami’in dan sanda mai kara Christopher John yace mai laifin ta batar da kudin da aka aike ta.

  "Lokacin da yayinyar ke kuka zuwa gida, wanda ake zargi wadda a gida daya suke, ya batra N200 sannan ya lalata ta a wani kangon gini. “Yarinyar ta je gida da kuka inda ta fadawa mahaifiyarta abunda ya faru.

  “An kai karar lamarin ofishin yan sanda sannan aka kama wanda ake zargin,” ya fadama kotu. Za’a ci gaba da sauraron karar a ranar 9 ga watan Satumba.
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu 
  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  Hausa.naij.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tsohon biri dan shekara 42 ya lalata ýar makwabcinsa mai shekara 11 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama