Samar da labarai ta intanet, yadda gwamnatin jihar Kebbi ta yi kasa a guiwa

Isyaku.com | 29-8-2018 |

Allah ya albarkaci jihar Kebbi da hazikan mutane daga ko wane bangare na jihar, amma wata babbar matsala da ke ci ma jihar tuwo a kwarya shi ne yadda kadan ne daga cikin wadannan hazikan mutane ke baje hazakarsu domin amfanin jama'a a wani bangare na fahimta.

Wani babban misali shi ne yadda jihar Kebbi ta wadatu da Profesa a kan harkar sadarwan zamani, amma fa shiru kake ji dangane da yadda wannan ilimi nashi zai amfani matasa da al'ummar jihar Kebbi, kusan haka yake a wasu sassa na ilimin zamani.

A bangaren aikin jarida kuwa, jihar Kebbi tana da wadatattu, kuma shahararrun yan jarida a fadin jihar, kamar wakilin gidan Talabijin na Liberty, Muryar Faransa, kuma tsohon wakilin gidan Rediyon Duetshe Welle, Leadership Hausa da sauransu. Amma duk da yawan wadannan 'yan jarida a jihar Kebbi, babu wata kafa ta watsa labarai ta intanet a zamanance a jihar Kebbi face ISYAKU.COM wanda yake da cikakken rijista karkashin Kampanin Seniora International.

Shafin gwamnati kwaya daya tilau baya da wani inganci da zai isar da sako ga jama'ar jihar Kebbi sakamakon yadda muka auna ayyukanta na tsawon wata biyu. Domin kimiyyar shiga shafin ya ci karo da yawancin irin wayar salula da yawancin jama'ar jihar Kebbi mazauna karkara ke amfani da shi domin shiga shafin yanar gizo. Sakamakon haka shafin ya rasa ingancisa wajen isar da sako ga al'umma.

Hakazalika, babu mawallafa ko marubuta shahararru da ake kira Online Publishers ko Bloggers a gaba dayan jihar Kebbi masu rijista, har ila yau dai sai ISYAKU.COM. Amma fa jihar Kebbi, kamar sauran jihohin kasar Arewa, tana da tarin yan Social Media masu kwasa suba a shafukan sada zumunta na Facebook ko WhatsApp.

Sakamakon haka ya sa jihar Kebbi ta kasance a baya wajen samar da ingantaccen rahoton labarai a shafukan yanar gizo, da yake Gwamnatin jihar Kebbi ba ta da shafin labaran yau da kullum a hukumance face tarin hotuna da ta sa wasu yan Social Media suke aikawa a zaurukan sada zumunta a intanet.

Bisa wannan tsari ma, hatta Uwargidan Gwamnan jihar Kebbi Dr. Zainab Bagudu, ta fi yawan isar da sakonta ta shafinta na Facebook, marmakin tsararren shafi da zai wadatar da masu karatu ta fannoni daban daban tun da shafin mai zaman kansa ne ta mashigar www ko http, watau daga ko ina a Duniya za a iya shiga shafin, amma idan a Facebook ne kawai, shi wanda baya amfani da Facebook ko kuma yana amfani da yar karamar wayar salula an baro shi a baya kenan.

Sau da yawa, Mawallafan shafuka kan sami kansu cikin yanayi na zama a tsakiyar Katanga sakamakon rashin fahimtar matsayinsu da yawancin yan Arewacin Najeriya ke yi. Shi Publisher ko Blogger mutum ne mai zaman kanshi ko dan jarida, ko masani wani fanni na ilimi wanda yayi rijista kuma sai ya fara watsa labarai, ko sakonni na ilimi, fadakarwa, ilmantarwa ko nishadantar ga al'mma.

Matsayin Mawallafi ko Blogger a tsarin aikatau na samar da bayanai ga jama'a ta intanet ba daidai bane da dan Social Media, domin dan Social Media baya da wani horo a kan abin da yake yi, watau ra'ayi ne kawai ko karambani. Amma shi Publishe ko Blogger masani ne a kan wani tsari na ilimi ko yanayi rayuwa ko kuma dan jarida mai zaman kansa.

Wani babban misali nassarar shafin ISYAKU.COM shi ne yadda ya zama ingantaccen kafa da al'ummar Masarautar Zuru da Yauri ke amfani da shi domin samun sahihan labarai da suka shafi jihar Kebbi, bisa dalilin cewa wannan bangare na jihar Kebbi da ke dauke da kananan hukumomi 7, aka baro su a baya tun 1991 da aka kirkiro jihar Kebbi daga jihar Sokoto. Domin wannan yanki basu da wadataccen wutan lantarki, ba kyakkyawar hanyar mota, ba ingantattu kuma wadatattun ruwan sha, ba gidan Talabijin, ba gidan Rediyo, kuma ba Asibitin kwarararru a kusa, sai an je Rijau ko Kontagora na jihar Niger ko Birnin kebbi.

Wanna lamari ya ja ma ISYAKU.COM daukaka ganin cewa jama'ar wannan yankin suna biye da shafin domin samar masu da labari bisa gaskiya na lamari da ake toyawa a jihar Kebbi.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN