• Labaran yau

  Sabuwar kungiyar wayar da kan matasan Darikar Tijjaniyya ta gudanar da wa'azi a Gwadangaji


  Isyaku Garba 18-8-2018


  Sabuwar kungiyar fadakarwa tare da wayar da kai ga matasan Darikar Tijjaniyya mai suna Tijanniya Youth Enlightenment Initiative ta gudanar da taron wa’azi domin tunatarwa bisa maudu’In muhimmancin neman ilimi a rayuwar matasan Musulmi. An gudanar da taron wa’azin a garin Gwadangaji da ke jihar Kebbi a daren Juma’a 17-8-2018.

  Wa ‘azin ya kunshi fadakarwa kan muhimmancin neman Ilimi wanda Malamam Tuhami Gwadangaji ya gabatar, tare da bayar da kissoshi da dama ,musamman ta wani Magidanci da ya rasa matarsa sakamakon jahilci, da sauran kissoshi da ya kawo daga Alqur’ani da litattafan ilimin addinin Musulunci.

  Hakazalika, Malam Rufa’I Liman Ambursa, nasiha ya yi kan Illolin shaye-shaye a cikin al’ummar Musulmi, musamman matasa. Malam Rufai, ya tabo kissoshi tare da misalai da dama, da ke tabbatar da zahirancin illolin shaye-shaye da hanyoyi da za’a kauce wa fadawa cikin ibtila’in shaye-shaye.

  Malam Mika’ilu Ibrahim, ya yi Karin haske ne tare da fadakarwa kan ka’idodi da sharuddan Darikar Tijjaniyya. Tare da bayar da misalai da dama da kuma yadda ya kamata dan Tijjaniyya ya kammala kanshi wajen tafiyar da Zikiri bisa ka’ida.

  Daga bisani kuma, Malam Abashi Zauro, ya yi nasiha ne game da Layya, sharudda, da ka’idodin yin Layya. Hakazalika ya kawo misalai da kissoshi da dama domin fadakarwa bisa yadda ya kamata a gudanar da Layya.

  Taron wa’azin na ranar Juma’a, ya sami albarkar halartar matasa Musulmi mabiya Darikar Tijjaniyya, hakazalika taron ya sami darajar bayyanar Manyan Malamai da kuma Dattijai kamar su Malam Mahmud Nura,Malam Garba Danjiya Gwadangaji, Malam Muhammad Liman Gwadangaji, Mal Liman Umaru Bargo, Malam Umaru Dankardi tare da shugaban Zakirai na Gwadangaji Alhaji Hantsi.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Sabuwar kungiyar wayar da kan matasan Darikar Tijjaniyya ta gudanar da wa'azi a Gwadangaji Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });