• Labaran yau

  Karanta yadda wata fusatacciyar budurwa ta dalla ma wata hafsar yansanda mari

  Wata fusatacciyar budurwa yar shekara 24 a birnin Lagos ta dalla wa wata hafsan yarsanda mari a cikin ofishinta bayan an kai budurwar ofishin hafsar yansandar mai suna DSP Laura Elo domin ta amsa tambayoyi kan kara da akayi a kanta.

  Amma ba wanda ya san ko miye ya biyo baya, sai dai abinda aka gani kawai shine yadda wannan budurwa ta dalla wa hafsar mari kuma ta zabura ta nufota domin a kece raini. Nan take aka shiga tsakaninsu. Wannan lamari ya faru a caji ofis na Ikeja a birnin Lagos.

  Bayanai sun ce tun farko dai, wata mata ce ta kai karar budurwar wajen yansanda dangane da wasu atamfofi da ta bata domin ta dinka, amma bayan an bata kudin dinki, sai budurwar ta kasa cika alkawari kamar yadda mai kara ta shaida wa yansanda, kuma sakamakon haka ne yansanda suka gayyato budurwar.

  Tuni dai yansanda suka gurfanar da ita a gaban wata Kotun Majistare a Ikeja. Bayan mai gabatar da kara na yansanda ya karanta mata tuhuma da ake yi mata, budurwar bata amsa laifinta ba , sakamakon haka Alkalin Kotun Mrs. O. Sule-Amzat ta dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 15 ga watan Nowamba.

  An bayar da belinta a kan N50.000, amma aka tasa keyarta zuwa Kurkuku kafin ta cika kaidodin beli.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karanta yadda wata fusatacciyar budurwa ta dalla ma wata hafsar yansanda mari Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });