• Labaran yau

  Kalli wani abin alhairi da Sanata Adamu Aliero ya yi wa jama'arsa. Hotuna

  Isyaku Garba |Birnin kebbi | 10-8-2018 |
  Hausawa sun ce kyaun alkawari cikawa, a wani yanayi na ganin kwakwap a kan ayyuka da Sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya Alh. Adamu Aliero ya yi a mazabarsa, isyaku.com ya yi tattaki domin gani da ido saboda a shaida ma Duniya gaskiyar lamarin.. Wadannan ayyuka, ya yi su ne a karamar hukumar Gwandu da Jega, kasancewa fuska ta farko a rahotun mu kan ayyukansa.

  *Ya tafiyar da shirin koya wa jama'a sana'oi a garuruwan karamar hukumar Gwandu, ciki har da Dalijan, Kambaza da sauransu.
  *Akwai kuma gini daya na Makaranta da ke dauke da dakuna 3 na karatu a garin Gwandu.
  *A garin Warari a Mazabar Zoramawa, mun gan Borehole 1 mai amfani da hasken rana da Sanata Aliero ya yi
  * Haka zalika mun gan fitilar haskaka titi mai amfani da hasken rana da Sanatan ya saka a Makarantar Allo na Kulliya da ke garin Gwandu.
  *Akwai kuma ginin makaranta mai dauke da dakuna 3 na ajin karatu wanda Sanatan ya gina.
  *A garin Gorkomodo kuwa, mun gan rijiyar borehole da ke amfani da hasken rana wanda Sanatan ya yi ma al'umma.
  *Haka zalika akwai ginin makaranta da ke dauke da dakunan karatu guda 3
  *Akwai kuma ginin makarantar Pramare daya da ke dauke da ajin karatu guda 3 wanda Sanatan ya gina a Alelu.
  *Akwai kuma wutar haskaka titi mai amfani da hasken rana da Sanata Aliero ya sa a Masallacin Markazissahaba a garin Jega.

  Za mu kawo maku cikakken jerin ayyukasa tun daga 2015 har zuwa 2018 da aka zabeshi zuwa Majalisar dattawa.   Ku kasance da sashen harkokin Siyasa na Mujallar isyaku.com domin ci gaba da kawo maku cikakken jerin ayyuka da Sanata Adamu Aliero ya kammala, karkashin garuruwa da yake wakilta a zauren Majalisar Dattawan Najeriya..

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu
  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli wani abin alhairi da Sanata Adamu Aliero ya yi wa jama'arsa. Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama