Jita-jitan sauke Faruku Inabo daga P.A na Gwamnan jihar Kebbi ba gaskiya bane

Isyaku Garba | 27-8-2018 |


Wani labari yana zagayawa a shafukan sada zumunta na Facebook da Whatsapp wanda ke nuna cewa Gwamnatin jihar Kebbi ta saukar da mai taimaka wa Gwamnan jihar watau P.A Faruku Inabo daga mukaminsa. Sakamakon bincike da Mujallar ISYAKU.COM ya yi, ya nuna akasin haka.
Wani Hadimin P.A Inabo ya shaida wa ISYAKU.COM cewa "wannan zancen ba gaskiya bane, domin ko ranar Juma'a ma Sakataren P.A Inabo ya yi aiki har zuwa karfe 11pm na dare domin tabbatar da kammala wasu ayyuka".

Gwamnatin jihar Kebbi dai bata ce uffan ba dangane da wannan jita-jita da ya yi karfi a fadin jihar Kebbi sakamakon yadda labarin ya yi saurin zagayawa a fadin jihar, wanda haka ya samo asali daga wani rikici da ya bulla tsakanin kungiyoyin BBSO da 4+4 kuma sakamakon haka ya sa Gwamnati ta rushe kungiyoyin.

Bisa ka'ida dai, idan haka ya faru, Gwamnati za ta fitar da sanarwa ta kafarta da aka saba domin muhimmancin kujerar P.A na Gwamna wanda ba lari ne na wasan yara ba.Sakamakon haka ya haifar da fahimtar rashin ingancin jita-jita da ke zagayawa a fadin jihar Kebbi dangane da lamarin.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN