• Labaran yau

  Dan takarar kujerar Gwamnan jihar Kebbi Ibrahim Nayelwa ya sami karbuwa ga Matasa - Hotuna

  Isyaku Garba | 24-8-2018 |


  Masarautar Dakingari
  Yayin da Kalangun Siyasa ya fara kadawa kuma dadin sautinsa ya zagaya sako-sako na jihar Kebbi, hakazalika an sami wasu da suka fara fitowa domin a taka rawar wannan kidain Kalangu na Siyasa tare da su. Domin dai wani matashi, kuma mai kishin jihar Kebbi, watau Alh Ibrahim Aliyu Nayelwa yana daya daga cikin yan takaran kujerar Gwamnan jihar Kebbi da a yanzu ya fito ya nuna aniyarsa a fili na neman kujerar Gwaamnan jihar Kebbi a shekara ta 2019.
  Masarautar Zuru
  Matashi kuma ma'aikacin Gwamnatin tarayyar Najeriya, Ibrahim Aliyu Nayelwa, ya yi amfani da hutun Sallar Layya, ya ziyarci wasu garuruwa a fadin jihar Kebbi, inda wani abin mamaki da ya gudana shi ne yadda wannan matashin ya sami karbuwa ga jama'a a garuruwan da ya ziyarta kamar Zuru,kuma ya sami tarbo daga Rafin Zuru, manyan Dattawa da yan Siyasar kasar Zuru, wadanda suka tabbatar mashi da amanarsu zuwa gareshi musamman Matasa.
  Garin Makera
  Hakazalika, Ibrahim A. Nayelwa, ya kuma ziyarci garuruwan Makera da garin Giwatazo, har da garin Maiyama inda ya zanta da jiga-jigan yan Siyasa, wanda a nan ma suka tabbatar mashi da amanarsu.
  Garin Zuru

  Wani abin mamaki shine yadda jama'a suka bayyana rashin jin dadin yadda Gwamnatin jihar Kebbi ke yin alkawari babu cikawa, yayin da wasu ke korafin cewa ko a zabe na 2015, sun yi shi ne a kan bashi ba a biya su ba har yanzu a karamar hukumar Maiyama, Zuru da wasu garuruwa da tawagar dan takaran suka ziyarta, domin isar da gaisuar Sallar Layya.
  Fadar Sarkin Suru

  Nayaelwa ya zana wasu daga cikin dalilai da suka sa ya masa kiran jama'a domin a raba su da Kado. Wasu daga cikin ababe da yake son ya yi gyara idan jama'a sun zabe shi a matsayin Gwamnan jihar Kebbi sun hada ada, kiwon lafiya, ilimi, samar da tsabtatattun ruwansha, samar da aiki tare da tallafi ga wadanda bbasu yi makaranta ba domin su yi amfani da wadannan kudade domin su tsaya kan kafafunsu.
  Garin Maiyama

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dan takarar kujerar Gwamnan jihar Kebbi Ibrahim Nayelwa ya sami karbuwa ga Matasa - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });