• Labaran yau

  Ciwon kafa ya kama matashin nan da ya je Abuja a kasa saboda Buhari

  A shekarar 2015 ne Abubakar Duduwale, masoyin shugaba Buhari, ya taka da kafar sa daga Yolan jihar Adamawa zuwa Abuja domin ya halarci rantsar da Buhari. Duduwale ya bayyana cewar ya yi tattakin ne domin nuna jin dadinsa da nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben shekarar 2015, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya Walla. Kafafen yada labarai da suka hada da gidan talabijin na kasa (NTA) sun nuna tattakin na Duduwale a ranar da ya bar Yola. Duduwale, dan kabilar Chamba daga karamar hukumar Yola ta Arewa, ya fara tattakin na shi ne daga kofar garin Yola dake kan babban titin Yola zuwa Numan da misalin karfe 6:30 na safe. Shekaru uku bayan ya yi wannan bajinta, Duduwale ya gamu da lalurar ciwon kafa kamar yadda hotunansa da suka mamaye kafafen sada zumunta suka tabbatar. Wani ma'abocin amfani da shafin sada zumunta na Tuwita @GASSA01 ya saka hoton Duduwale tare da bayyana cewar yanzu haka ya nakasa kuma yana matukar neman taimako. Read more: https://hausa.naija.ng/1184731-wayyo-ciwon-kafa-ya-kama-matashin-nan-da-ya-je-abuja-a-kasa-saboda-buhari.html#1184731
  A shekarar 2015 ne Abubakar Duduwale, masoyin shugaba Buhari, ya taka da kafar sa daga Yolan jihar Adamawa zuwa Abuja domin ya halarci rantsar da Buhari.

  Duduwale ya bayyana cewar ya yi tattakin ne domin nuna jin dadinsa da nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben shekarar 2015, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya Walla.

  Kafafen yada labarai da suka hada da gidan talabijin na kasa (NTA) sun nuna tattakin na Duduwale a ranar da ya bar Yola. Duduwale, dan kabilar Chamba daga karamar hukumar Yola ta Arewa, ya fara tattakin na shi ne daga kofar garin Yola dake kan babban titin Yola zuwa Numan da misalin karfe 6:30 na safe.

  Shekaru uku bayan ya yi wannan bajinta, Duduwale ya gamu da lalurar ciwon kafa kamar yadda hotunansa da suka mamaye kafafen sada zumunta suka tabbatar. Wani ma'abocin amfani da shafin sada zumunta na Tuwita @GASSA01 ya saka hoton Duduwale tare da bayyana cewar yanzu haka ya nakasa kuma yana matukar neman taimako.  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu 
  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  Hausa.naij.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ciwon kafa ya kama matashin nan da ya je Abuja a kasa saboda Buhari Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama