• Labaran yau

  Zafin kishi ya sanya wata matar basarake kashe ‘yar kishiyarta


  Rundunar ‘yan sanda ta jihar Osun ta cafke wata matar wani basaraken gargajiya yau Alhamis tare da karin wasu mutane biyu bisa zargin cinnawa gidan kishiyarta wuta wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar ‘yar kishiyar mai shekaru 3 a gabarar.

  Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Olafimihan Adeoye ya bayyana cewa mijin wacce ake zargin wanda basaraken gargajiya ne mai suna Oba Morufudeen Olawale ne ya kai karar faruwar lamarin ga hukumar. Oba Morufudeen dai shi ne mai rike da sarautar Alabudo a Abudo dake karamar hukumar Egbedore ta jihar Osun. Basarake Adeoye ya ce matar tasa da ake zargi tare da wadansu abokan shedancin nata biyu ne suka baro gidajensu suka je unguwar Ede ta yankin Abudo inda gidan daya matar tasa take tare da ‘yarta takanas suka cinna wutar da misalin karfe 1:00am na dare, a ranar 6 ga watan Yunin da ya gaba ta.

  A sakamakon hakan ne hayaki ya yiwa ‘yar yarinyar illar har ta ce ga garinku nan, yayin da ita ita kuma mahaifiyar yarinyar ta samu mummunan rauni.

  Kwamishinan ‘yan sandan na jihar ya shaida cewa yanzu haka tana can asibiti tana karbar magani Sannan ya ce binciken ‘yan sanda dai ya nuna cewa matar da ta cinna wutar ita ce matar basaraken ta uku yayin da wadda aka cinnawa gidanta wuta kuma take ta hudu. Kuma ya ce da zarar an kammala bincike za’a mika matan uku da ake zargi domin girbar abinda suka shuka. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.
   

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

  hausa.naij.ng
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Zafin kishi ya sanya wata matar basarake kashe ‘yar kishiyarta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });