Rundunar yansandan jihar Kebbi ta gabatar wa manema labarai wani Bafulace mai suna Babuga Kuaara wanda ake zargin ya kashe wani safeton yansanda Umaru Danladi da ke aiki a ofishin yansanda na garin Ka'oje a karamar hukumar Bagudo na jihar Kebbi.
Safeto Umaru Danladi ya gamu da ajalinsa ne a hannun Babuga, bayan safeton ya je domin ya gayyace shi bafulacen bisa kara da aka shigar a kansa cewa ya kora dabbobi sun yi barna a gonar wani manomi.
Amma yayin da suke kan tafiya domin safeton ya kai shi wajen motar yansanda da take jira a bakin hanya, sai Babuga ya zare adda ya sare safeto a wuya wanda sakamakon haka ya mutu domin jini da ya zuba matuka.
Kwamishinan yansandan jihar Kebbi Ibrahim Kabiru, ya ce rundunarsa za ta gurfanar da Babuga a gaban Kotu.