• Labaran yau


  Wasu 'yan ta'adda sun tuba ga Allah sun mika makamai a kudancin Najeriya - Hotuna

  An wayi gari cikin farin ciki a garin Port Harcourt na jihar Rivers, bayan wasu dimbin matasa da suka dade suna addabar wannan yankin da harkokin kungiyoyin asiri suka tuba kuma suka mika makamansu ga 'yansanda.

  Matasan sun yi haka ne a gaban shugaban wata Mujami'a David Ibiyeomie na Cocin Salvation Ministries, wanda daga bisani ya shigar da su makarantar koyon Addinin Kiristanci.

  Bayanai sun ce bayan matasan sun kammala makarantar za a taimaka masu da abin dogara a rayuwa.

  Haka zalika , matasan sun mika makamansu ga hukumar 'yansanda na jihar Rivers


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wasu 'yan ta'adda sun tuba ga Allah sun mika makamai a kudancin Najeriya - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama