• Labaran yau

  Talauci ne ya sa ni, yar shekara 20 da ke kashe bil'adama a kan N10.000

  Mahaifiyata ta bukaci in yi aure, amma wanda ya fito neman aure na wani tsoho ne, sakamakon haka na bi wata kawata zuwa birnin Lagos inji wata fitacciyar yar kungiyar asiri ta Yarbawa Eiye confraternity. Maryam Abiola yar shekara 20 ta yi fice wajen kisan bil'adama a cikin kungiyar asirin musamman a unguwar Ilesamaja na birnin Lagos, wajen da aka kama ta da sauran yan kungiyar a maboyarsu.

  Maryam ta ce bayan zuwanta Lagos, ta fuskaci matsin rayuwa wanda ya sa ala tilas ta fara sayar da piyawata, daga bisani kuma ta fara karuwanci domin ta sami abin rayuwa.

  Ana cikin haka ne ta gamu da wani mai suna Saddiq wanda ya jawo hankalinta domin ta shiga kungiyarsu ta asiri, daga karshe ta aminta domin ita bata taba ganin N10.000 ba a rayuwarta, sakamakon haka Sadiq ya bukaci ta shiga wani gida ta kashe wata tsohuwa da Sadiq ya ce muguwar tsohuwa ce sakamakon haka ta cancanci mutuwa.

  Maryam ta ce ta shiga gidan wannan tsohuwa da dare ta tarar tana barci tare da yaranta, sai ta yi amfani da bindiga da Sadiq ya koya mata yanda ake aiki da shi ta harbe tsohuwar har lahira, sai ta ruga ta kai ma Sadiq bindigar. Washe gari kuma sai ta dawo da safe domin ta tabbatar cewa wannan tsohuwar ta mutu.

  Maryam tana cikin dimbin yan kungiyar asiri da yansanda suka kama a unguwar Ilesamaja da ke birnin Lagos mako da ya gabata, kuma ana gudanar da bincike.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Talauci ne ya sa ni, yar shekara 20 da ke kashe bil'adama a kan N10.000 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });