Majalisar Dattawa ta Najeriya ranar Talata, ta kayyade wa'adin mako biyu domin ta yi kwaskwarima ga kundin tsarin mulki na 1999 domin ta bayar da damar yiwuwar samar da 'yansandan jihohi saboda tunkarar matsalar tsaro a fadin kasarnan.
Daruruwan 'yan Najeriya ne suka rasa rayukansu sakamakon fadace-fadace tsakanin al'umma musamman Manoma da Makiyaya.
Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya ce "Majalisar Dattawa ta umarci kwamitin bita ga tsarin mulki domin ta samar da matakai da za su kai ga yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki da zai bayar da dama jihohi su kirkiro 'yansandan jihohi".
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira