• Labaran yau

  Kalli wannan fa ba budurwa ba ce, dan daudu ne mai hazaka - Hotuna

  isyaku.com

  Wannan hoto wani dan daudu ne mai hazaka, sunanshi Okuneye Idris Olarenwaju, amma amfi sanin shi da suna Bobrisky. Shi dai wanan dan daudu, mutum ne da ya dade yana fadi tashi domin ganin ya bullo da wani abu da zai taimaka wa rayuwarsa wajen dogaro da kanshi.

  Ana cikin wannan yanayin ne sai Bobrisky ya gano cewa mata sun fi son a ce suna da hasken fata, sakamakon haka fa gogan naka ya shiga bincike akan yadda zai hada sinadari da zai sa fata ta yi haske.

  Bayanai sun nuna cewa gogan naka ya taba hada wani sinadarin hasken fata, sai ya gwada a jikinsa, nan take fa wannan bangare ya kone, har fa Bobrisky ya yi jinya. Ammam haka bai hana shi dagewa ba domin ci gaba da nazarin wasu sinadarai.

  Daga karshe dai Bobrisky ya gano kuma ya hada wani sinadari mai sa fata ta yi haske tswal,kuma babu alamar baki a yatsu ko guiwa. Sai dai fa gogan naka yana diba wannan mai ne a kan N250.000. Kuma 'yan mata wadanda suka amsa sunan mata suna yawan sayen wannan mai na Bobrisky.

  DARASI

  Shi dai wannan Bobrisky Bayarbe ne, amma kalli yadda ya kirkiro hanya da zai dinga samun kudin rufin asiri sabanin yadda yan daudun kasar Hausa suka zama wasu ababen ban haushi da kyama a cikin al'umma.

  Ga raini, wai shi dandaudu, ga cin mutunci ga wanda ba dan daudu ba wai domin kada a rainashi, saboda shi dan daudu ne da ya fi son a kira shi mace kuma fa ga shi da gemu har da saje.

  Allah ya sauwake ya kuma kiyayemu.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY Latsa nan domin ka sauke Manhajarmu ISYAKU.APK https://docs.google.com/uc?export=download&id=0B7lmLLhGZSx5OTVENFlsTkllRTQ Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli wannan fa ba budurwa ba ce, dan daudu ne mai hazaka - Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });